<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Wannan bishara kuwa ta mulki
 Za'ayi wa'azinta ga duniya.
 Domin shaida ga dukan al'ummai
 Sa'annan mutuƙa za ta zo.

[V2]
 KORUS
 Sa'annan, sa'annan, matuƙa, matuƙa
 Sa'annan matuƙa za ta zo.
 2) Gama kamar walƙiya daga gabas
 Kuna ganinta kuwa bar yamma.
 Haka nan Ɗan mutum za ya zo.
 Sa'annan mutuƙa za ta zo.
 Korus
 3) Daga itacen ɓaure ku ga ne
 Sai ku koyi misalinsa
 Sa'anda yana hudo ganyensa
 Sa'annan mutuƙa za ta zo.
 Korus
 4) Ku tuna da zamanin Nuhu ƴan'uwa
 Ya sha ba'a cikin aikinsa
 Amma ya ci gaba da yin jirginsa
 Sa'annan matuƙarsu ta zo.
 Korus
 5) Sai mu jimre da aikin bishara
 Har dukan duniya ta tsira
 Domin Yesunmu yana zuwa
 Sa'annan matuƙa za ta zo.
 Korus
 6) Yesu zai karɓe mu cikin sama.
 Cikin gidan Ubansa.
 Rawanin Rai yana jiranmu.
 Sa'annan matuƙa za ta zo.</lyrics>
<title>Sa’annan Matuƙa Za Ta Zo LW508</title>
<hymn_number>508</hymn_number>
</song>